Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan takara a jihohin Adamawa da Taraba sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya


Zaben 2015 a Najeriya. )
Zaben 2015 a Najeriya. )

'Yan takara karkashin dukkan jam'iyun siyasa a jihohin Adamawa da Taraba, arewa maso gabashin Nigeria sun rattaba hannu akan yarjejeniyar tabbatar an gudanar da zabe, ba tare da tashin hankali ba.

'Yan takarar gwamna a jihohin Adamawa da Taraba sun rattaba hannu akan yarjejeniyar tabbatar an gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa, Mr Gabriel shine ya karanta yarjejeniyar a gaban kwamishinan hukumar zabe na jihar.

Dukkan yan takarar sunce yarjejeniyar tana da muhimmanci, kuma sun baiyana fatar za'a gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba.

Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta INEC a jihar Alhaji Baba Abba yace hukumar zabe ta shirya tsaf, domin jama'a suje su kada kuri'arsu a ranar Asabar idan Allah ya kaimu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG