Janar Buhari yace yana neman shugabanci ne saboda mutane dake ganin zai iya tabuka wani abu akan inganta tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da talauci.
Janar Buhari wanda ya sake shiga yarjejeniya da Shugaba Jonathan kan tabbatar da lumana da zaman lafiya yace magoya bayansa ka iya kula da kuri'unsu bisa ga tanadin doka. Yace abun da ya dinga fadi tun daga 2003 da ya shiga zabe shi ne a kasa a tsare a raka. Yace wannan halal ne ga duk masu kada kuri'a.
Yace cewa suka yi idan mutum ya kada kuri'a ya koma jefe daya ya jira a bada sakamako kana yayi tafiyarsa. Ko sanda bai kamata kowa ya je da ita rumfar zabe ba.
Buhari yace rashin yakamata ne wai wasu na sayar da katunan zabensu. Yace ya ji daga Muryar Amurka. An yiwa wasu tambayoyi kuma sun yadda sun sayar da katunansu wai domin su biya bukatun kansu saboda talauci da kuma mutuwar zuciya.
Wani mai goyon bayan Janar Buhari Muhammad Inuwa Yahaya yace tunda Buharin ya tsallake kalubale daban daban shi ne yake da tagomashin lashe zaben. Jama'ar kasar sun nuna Buhari suke so. Yace zasu ja har zuwa koina su tabbatar da nasarar Buhari.
To saidai Ahmed Gulak tsohon mai baiwa shugaba Jonathan shawara yana ganin har yanzu 'yan adawa basu shirya karbar ragamar mulki daga hannun Jonathan ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.