Gwamnan ya kira matasa kada su bari wasu 'yan siyasa su yi anfani dasu wurin cimma nasu burin.
Gwamnan yace abun da baka da iko a kansa babu yadda zaka yi dashi. Haka kuma abun da zaman lafiya bai baka ba tashin hankali ma ba zai baka ba. Yace duk wanda ya kira matasa ya basu kudi domin su ci mutuncin wani su karbi kudin amma su rokeshi ya hadasu da nashi dan da ya haifa su je tare su yi.Idan bashi da da a gaya masa ya hada da kaninsa. Idan ya kasa yin hakan to ba masoyi ba ne sai a yi watsi dashi. Irin wannan dan siyasan ba mai son cigaban al'umma ba ne.
Gwamnan ya cigaba da gayawa matasan Kaduna da duk jama'ar jihar cewa ba za'a iya canza hukuncin Ubangiji ba. Yace kamata yayi su bi Allah a hankali su roki alheri gareshi shi ya fi alheri da neman yin komi cikin fitina.
Yace rai daya ne. Sabili da haka bai kamata a ce wani ya rasa ransa kai ka rayu ba. Bai kamata a ce a kashe wani ba ko a tunzura mutane su kashe wani ba.
Gameda kada kuri'a gobe gwamnan yace ya kamata kowa yayi an fani da 'yancinshi. Kowa yayi ra'ayinsa. Kowa ya zabi abun da yake so. Doka bata ba kowa daman hana wani ra'ayinsa ba.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara.