Jam'iyyar APC da wasu jam'iyyu suna haramar zuwa kotu akan zargin cewa an tafka magudi a wasu wurare a jihar. Zasu kalubali jam'iyyar PDP game da sakamakon zaben.
Jam'iyyun basu amince da samun nasarar PDP ba game da wasu kujerun 'yan majalisar dattawa da na wakilan tarayya.
APC na zargin an yi mata aringizon kuri'u a wasu mazabun jihar. A taron manema labarai da jam'iyyar ta kira shugabanta Alhaji Jika Ardo ya bayyana cewa akwai wurare a Wukari da aka yi magudi. Yace a Wukari an dauko kuri'un ne aka zauna cikin gida ana dangwalasu ba wai mutane ne suka kada kuriun ba. Yace ina ne PDP ta samu mutane dubu sittin da hudu a Wukari.
Kodayake wakilinmu bai samu ya zanta da shugabannin PDP ba saboda wasu dalilai da suka fi karfinsa amma ya zanta da wasu 'yan takarar PDP wadanda suka musanta zargin da APC ke yi. Shehu Marafa Abba da ya lashe kujerar sanata a Taraba ta tsakiya yace kam sun godewa Allah. Ya kira wadanda ya tsaya dasu su yi hakuri domin komi na kan lokaci.
Alhaji Muhammad Danburam daya daga cikin masu sa ido a zaben yace kotu zata yi magani amma kowane dan takara ya tabbatar cewa abun da wakilinsa ya bashi abun da ya gani ne ya kuma gaskanta kana ya yi anfani dashi a kotu.Kada ya je ya bata ma kansa lokaci ya kuma bata lokacin jama'a a kotu. Idan an je a duba zargin kuma babu, to ya yi aikin banza.
Amma Malam Kabiru Jalingo yace a je kotu domin zaben bai yi ba a wasu wuraren. Idan kotu zata yi gaskiya za'a warware matsalolin.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.