Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Bom na Biyu a Nyanya


Masu agajin gaggawa a birnin Tarayya Abuja.
Masu agajin gaggawa a birnin Tarayya Abuja.

​Babban darektan hukumar agajin gaggawa ta babban birnin tarayyar Najeriya, Abbas Garba Idris ya ce mutane 19 ne suka rasa rayukan su sanadiyar fashewar wata motar boma-bomai a tashar motocin safa da ke bayan garin babban birnin na Abuja.

'Yan Sanda sun ce mutane masu dimbin yawa sun ji ciwo da yammacin jiya Alhamis cikin fashewar wadda ta wakana daf da inda boma-bomai suka tashi a ranar 14 ga watan Afrilu a tashar motar har mutane 75 a kalla suka halaka.

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin na watan Afrilu. Amma babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin jiya.

Najeriya na shirin karbar bakuncin babban taron kolin tattalin arzikin da za a yi makon gobe a kan nahiyar Afirka. Shugaba Goodluck Jonathan yayi alkawarin baiwa taron gagarumin tsaro na musamman.

A jiya Alhamis Mr. Jonathan ya fada cewa Najeriya za ta yi nasara a kan mugun nufin da ke neman tozarta bil Adama.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG