Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bam Ya Fashe a Nyanya Kusa da Abuja


Mutane sun taru a inda Bom ya fashe a tashar motar haya ta Nyanya, kilomita 16 daga tsakiyar birnin Abuja, Najeriya, Afrilu 14, 2014.
Mutane sun taru a inda Bom ya fashe a tashar motar haya ta Nyanya, kilomita 16 daga tsakiyar birnin Abuja, Najeriya, Afrilu 14, 2014.

Rahotanni da dumi duminsu sun tabbatar da fashewar wani bam a wata tashar mota a Nyanya kusa da Abuja, a Najeriya.

Wani bam ya fashe a Nyanya kusa da Abuja da safen nan waje jen karfe bakwai lokacin da mutane ke hada-hadar shiga motoci zuwa aiki.

Jummai Ali Maiduguri ta zanta da wakilin Muryar Amurka, Saleh Shehu Ashaka wanda ya tabbatar da fashewar bam a tashar mota da mutane ke shiga motoci zuwa Suleja da Minna da wasu wurare. Yanzu dai an tabbatar da mutuwar akalla mutane ashirin yawancinsu ba'a iya ganesu.

Mutane da dama sun rasa rayukansu har ma ana kwasan wadanda bam yayi raga-raga dasu cikin wilbaro. Motoci fiye da ashirin suka kone kuma wasu ma na cin wuta lokacin wannan rahoton.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin dasa bam din.

Ga rahoto.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG