Shugaba Jonathan yayi kiran ne ta bakin ministan labarai Labaran Maku wanda ya wakilceshi a wajen bikin cika shekaru dari da haihuwar shi Olubadan.
Shugaban na Najeriya ya cigaba da cewa suna garin Ibadan din ne domin yin bikin shekaru dari na rayuwar mutum mai daraja, mai haskakawa, sarki cikin sarakuna mai shugabanci da misali mai kyau, mai son zaman lafiya da kaunar cigaba.
Jonathan ya nuna rashin jin dadinsa da rasa kasancewa da kansa wurin bikin sabili da fashewar bamabamai a Nyanya kusa da Abuja. Yace duk da yawan shekarun Olubadan yayi kokarin hada kan jama'arsa.
Shi ko gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ya bukaci 'yan Najeriya da su kaunaci juna duk da banbancin addini ko kabila. Gwamnan yace jama'ar Ibadan suna cike da murna da ganin wannan rana.
An haifi Olubadan din ne ranar 14 ga watan Afrilu shekarar 1914 a Igbo Elerin dake karamar hukumar Lagelu. Ya rike masarautu iri daban daban kafin ya zama Olubadan ran 17 ga watan Augusta a shekarar 2007 kuma shi ne Olubadan na farko da ya cika shekaru dari da haifuwa yana karagar milki.
Bikin ya samu halartar kusoshin gwamnatin tarayya da na jihohi, 'yan kasuwa, kungiyoyi, sarakuna da dai sauransu.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.