ABUJA, NIGERIA - INEC dai ta sha suka daga manyan jam’iyyun hamaiya na PDP da Leba da rashin tura sakamako ko baiyana sakamakon da a ka tattara daga na’urar ta BVAS a lokacin zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan jiya.
Hukumar zaben wacce ta dage zaben jihohin daga makon jiya zuwa wannan mako, ta yi aikin saita muhimman bayanai don zaben kamar taken zaben da kuma kwanan wata.
INEC ta ce kowace rumfa na mallakar na’urar kuma za a kawo karshen duk kalubalen da a ka fuskanta wajen sarrafa na’urar don samun mafi sahihancin sakamako.
Jami’a a sashen labarun hukumar Zainab Aminu ta ce hukumar na bukatar duk masu zabe su fito su kada kuria’r su da tabbacin samun sakamako daga na’urar da a ke yi wa kirari ta na taimakawa wajen yaki da magudi.
In haka ne me ya dace bisa doka masu zabe su yi matukar INEC ba ta cika alkawarin ba.
Barista Musa Adamu wani lauya mai zaman kan sa a Abuja ya ce ba zabi bayan ayyana sakamakon zabe sai tafiya kotu musamman in masu zaben sun tabbatar yawan kuri’un da su ke zargin an murde za sui ya sauya sakamakon zaben daga na wanda a ka aiyana ya lashe.
Alhaji Umar Gital wani daga ‘yan siyasar da zabe ba ya wuce su tun 1999, ya ce ba mamaki in sabuwar na’ura ta samu tutsu kafin a gwanance da aiki da ita.
Dan takarar adawa a NNPP a Bauchi Halliru Dauda Jika ya yi fatan na’urar za ta yi aiki kamar yanda a ka yi alwashi.
A yanzu haka PDP da Leba na shirya shaidu don gurfanar da hukumar zabe gaban kotu kan zargin keta haddin aiki da BVAS.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-HIkaya: