Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Sauya Babban Baturen Zabe A Sokoto


Taron Hukumar INEC Da Kungiyoyin Sa Ido Kan Zaben
Taron Hukumar INEC Da Kungiyoyin Sa Ido Kan Zaben

Daukan wannan mataki na zuwa ne yayin da ya rage 'yan kwanaki a gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a wasu jihohin kasar.

Sa’o'i 48 bayan da shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya lashi takobin hukunta jami’an hukumar masu sakaci, tuni ya fara cika wannan alkawari.

A wani taron da ya yi da manyan turawan zaben jihohi a ranar Asabar, Yakubu ya yi wa jami’an hukumar gargadi sannan ya sha alwashin cewa duk wasu daga cikin su ba za su kasance cikin masu aikin zabe mai zuwa na gwamnoni da ‘yan majalisu jihohi ba wanda za a gudanar a ranar Asabar 11 ga wannan watan nan na Maris , bisa zargin wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar shugaban na INEC ya ce “yayin da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi yake dada matsowa, ya zama wajibi mu dada zage dantse domin shawo kan kalubalolin da muka fuskanta a zaben da ya gabata. ‘Yan Najeriya ba za su amince da wani abu sabanin wannan ba”.

Ya kuma kara da cewa, “duk wani jami’in da aka kama da yin sakaci da aikinsa ba zai yi aikin zaben ba, ban kuma ware kowa ba, har da manyan turawan zabe."

A wata wasika mai sanye da kwanan watan jiya Litini 6 ga watan Maris dauke da sa hannun sakataren hukumar Rose OriaranAnthony, INEC ta yi wa sakataren gudanarwar Hukumar Hauwa’u Kangiwa Umarnin kula da ofishinta na Sokoto ba tare da bata lokaci ba.

Sannan, ya yi wa babban baturen zaben na Sokoto da ya kauracewa ofishin hukumar ba tare da bata lokaci ba.

“Umarnin da aka yi wa sakataren gudanarwar ya bukaci ta kula da dukkanin ayyukan hukumar a ofishin na sakwato ba tare da bata lokaci ba”.

A wata wasikar kuma an bukaci Kangiwa ta yi aiki tare da kwamishana mai kula na hukumar ta kasa, Farfesa Muhammad Sani Kala, har zuwa lokacin da za a sake tuntubar ta.

XS
SM
MD
LG