Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Najeriya Ta Dage Zaben Gwamnoni Da Na Majalisar Jiha Da Mako Guda


Zaben Najeriya
Zaben Najeriya

Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta dage gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha zuwa ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Hukumar INEC ta dauki matakin ne don samun damar saita na'urorin BVAS da ke kunshe da alkaluman zaben shugaban kasa da majalisar tarayya, wanda aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Bayan wani taro da jam'iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki kan harkar zabe ne INEC ta dage zaben da ta shirya gudanarwa ranar Asabar 11 ga watan Maris, da kuma umurnin kotu na ba da dama ga jam’iyyun PDP da Labour su duba na'urar don tattara bayanan kalubalantar ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Kotun daukaka kara ta bai wa INEC hurumin shirya zaben na jiha, amma kuma hukumar ta tabbata ta adana dukkan bayanan sakamakon zaben shugaban kasa a babbar ma'adanar bayananta.

An Kama Wani ‘Dan Jam’iyyar APC Da Katunan Zabe Fiye Da 300 A Jihar Kano
An Kama Wani ‘Dan Jam’iyyar APC Da Katunan Zabe Fiye Da 300 A Jihar Kano

Jami'a a sashen yada labarai ta hukumar INEC Zainab Aminu, ta ce za a adana duk bayanan da kowacce jam'iyya zata bukata.

Daya daga cikin daraktan yakin neman zaben Peter Obi na jam'iyyar Labour Ibrahim Abdulkarim, ya ce tuni suka fara aikin duba na'urar ta INEC da samun bayanai masu muhimmanci.

Shugaban jam'iyyar ACCORD Muhammad Lawan Nalado, ya ce tun a lokacin taron daukar matakin wasu suka fara tsegunta wa na bayan fage halin da a ke ciki.

Hukumar INEC ta bai wa 'yan takara damar ci gaba da kamfe har zuwa gab da zabe a makon gobe.

XS
SM
MD
LG