Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Kara Daukan Tsauraran Matakai A Yankunan Da Ke Karkashin Dokar Ta Baci A Nijar


Janar Abdourahmane Tiani, Niamey, Niger Yuli 28, 2023. Picha na REUTERS/Balima Boureima.
Janar Abdourahmane Tiani, Niamey, Niger Yuli 28, 2023. Picha na REUTERS/Balima Boureima.

Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta bayyana shirin karfafa matakan tsaro a yankunan da ke karkashin dokar ta baci, bayan la’akkari da yadda ‘yan ta’adda suka zafafa kai hare-hare a ‘yan kwanakin nan.

Saboda haka aka gargadi jama’a da su bi umarnin hukumomi da na jami’an tsaro don ganin an cimma nasarar sabbin matakan tsaron da za su biyo baya.

Jerin hare-haren da aka fuskanta daga ranar Lahadi 15 ga watan Satumba zuwa ranar Larabar 18 a jihohin Tilabery, Diffa da Tahoua, ya haddasa asarar rayukan sojoji sama da 10.

Gwamnatin mulkin sojan Nijar, wacce ta saurari bahasi daga ministan tsaron kasa, Janar Salifou Mody, a taron majalisar ministoci na yammacin ranar Alhamis, ta ce wannan aika-aika da ke faruwa a daidai lokacin da ake cika shekara 1 da kafuwar kungiyar AES, yunkuri ne na kaste wa kasashen yankin hanzari a ayyukan ci gaban da suka dukufa a kai.

“Hasali ma makarkashiya ce da abokan gaba suka kitsa da nufin rikita al’amura a wadanan kasashe saboda haka ya zama wajibi a tsaurara matakan tsaro a karkashin dokar ta bacin da gwamnatin ta kafa a watan ogustan 2024,” in ji ta.

Abdourahamane Alkassoum, mai sharhi ne kan sha’anin tsaro ya ce halin da ake ciki a yau a Nijar da makwabta ya kai matsayin da za a dauki irin wannan mataki.

An dai bukaci al’umma ta bai wa hukumomi da jami’an tsaro hadin kai don ganin an zartar da sabbin matakan da za a shimfida a nan gaba ba tare da wata tangarda ba.

Shugaban kungiyar makiyayan arewacin jihar Tilabery Boubacar Diallo ya yi na’am da wannan tsari, ko da yake kuma a cewarsa abin na bukatar gyara.

Tun a farkon watan nan na Satumba ne jami’an tsaro suka kaddamar da ayyukan sintiri da binciken ababen hawa a manyan biranen Nijar mai lakanin Operation tsaron kasa da nufin tabbatar da tsaron cikin gida.

Yayin da alamu ke nunin abubuwan da suka wakana a farkon mako da ya wuce a jihohin Diffa, Tilabery da Tahoua da daya gefe farmakin ta’addancin da aka kai a birnin Bamako na kasar Mali sun sa hukumomin tsaro kara jan damara a ciki da kewayen birnin Yamai.

Saurari cikikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG