Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Diflomasiyya Tsakanin Nijer Da Benin Da Batun Tsaro Na Barazanar Ga Aikin Batutun Man Niger


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Bututun mai da China ta shirya, wanda zai maida Nijar kasa mai fitar da man fetur na fuskantar barazana sakamakon matsalar tsaro a cikin gida da kuma takaddamar diflomasiyya da makwabciyarta Benin, biyo bayan juyin mulkin bara wanda ya hambarar da gwamnatin dimokaradiyyar kasar ta Afirka ta Yamm

Bututun mai tsawon kilomita 1,930 (meli 1,200) ya taso ne daga rijiyar mai na Agadem da kasar China ta gina a Nijar zuwa tashar ruwan Cotonou na kasar Benin. An tsara shi ne domin taimakawa kasar Nijar mai arzikin man fetur amma bata teku, ta samu karuwar yawan man da ake hakowa kusan sau biyar, ta hanyar yarjejeniyar dala miliyan 400 da aka kulla a watan Afrilu da kamfanin mai na kasar China.

Sai dai yarjejeniyar ta fuskanci kalubaloli da dama, ciki har da rashin jituwar diflomasiyya da Benin da ta kai ga rufe bututun man a makon da ya gabata. Har ila yau, an kai wani hari a cikin wannan mako na kungiyar 'yan tawayen Patriotic Liberation Front, wadda ta yi ikirarin kashe wani bangare na bututun mai tare da yin barazanar kai wasu hare-hare idan ba a soke yarjejeniyar dala miliyan 400 da China ba.

Kungiyar karkashin jagorancin Salah Mahmoud, tsohon madugun 'yan tawaye, ta dauki makamai bayan juyin mulkin soji a Nijer, lamarin da ya kara yin barazana ga tsaro a kasar, wadda tuni ke fama da matsalar tsaro.

Masu sharhi na ganin cewa rikicin na iya kara yin illa ga kasar Nijar, daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya da ke samun mafi yawan kasafin kudinta daga tallafin waje da yanzu aka hanata biyo bayan juyin mulkin kasar.

A halin yanzu Nijar na da karfin tace ganga 20,000 kacal a kowace rana don bukatun cikin gida yayin da bututun zai fitar da ganga 90,000 a kowace rana, wata nasarar da jami'ai da manazarta suka ce zata taimaka wa kasar wajen habaka kudaden shiga da kuma fita daga cikin takunkuman juyin mulkin da suka mayar da ita saniyar ware daga makwabtan yanki da kuma suka cutar da tattalin arzikinta da al'ummarta.

Wani babban abin damuwa shi ne yadda dakatar da aikin bututun man zai yi tasiri ga ci gaban tattalin arzikin Nijar baki daya. Bankin duniya ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Yamma zai farfado kuma zai bunkasa cikin sauri a nahiyar Afirka a bana da kashi 6.9%, tare da fitar da mai a matsayin wani muhimmin ci gaba.

Rikicin diflomasiyya da Benin ya samo asali ne tun a watan Yuli lokacin da aka hambarar da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum a wani juyin mulki, lamarin da ya sa kasashen yammacin Afirka da ke makwabtaka da Nijar suka rufe kan iyakokinsu da Nijar, da kuma kafa kungiyar nan mai ikirarin 'yantar da yankin da a yanzu ke barazanar kai wasu hare-hare kan aikin man.

Kasar Benin tare da wasu kasashe makwabta sun sake bude kan iyakarsu da Nijar, amma jami'an Nijar sun ki bude nasu, suna masu zargin kasar Benin da karbar bakuncin sojojin Faransa da ke barazana ga kasar bayan Nijar ta yanke huldar soji da Faransa. Hakan ne ya sa shugaban kasar Benin, Patrice Talon ya sanya sharadi na sake bude iyakokin kasar da fitar da man ta tashar ruwanta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG