Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Sojojin Nijar 12 Ne Aka Kashe A 'Yan Kwanakin Bayan Nan


Sojojin Nijar
Sojojin Nijar

Dakarun sojin sama da na kasa sun kashe sama da maharan har su 100, bisa bayanan sojojin ba tare da wani karin bayani ba.

Wani labari da kamfanin yada labarai na AP ya wallafa ya ce, wasu hare haren kwanton bauna da fashewar wasu abubuwa a fadin Nijar da ke karkashin mulkin soji ya kashe akalla sojoji dozen guda, sannan wasu 30 kuma sun jikkata da a cewar hukumomin sojin kasar cikin wata sanarwar da aka yada ta kafar talabijin din kasar ta Nijar a ranar Laraba.

A harin farkon da aka kai yankin yammacin Tillabery a ranar Lahadi, wani gugun(ayari) masu aikata laifuka da suka shiga garin ne suka kashe sojoji 5 sannan wasu 25 kuma suka jikkata, abin da sojoji suka sheda kenan.

Dakarun sojin sama da na kasa sun kashe sama da maharan har su 100, bisa bayanan sojojin ba tare da sun yi wani karin bayani akan su ba.

A ranar Litinin kuma a yankin kudu maso yammacin Diffa, inda ake yawan kai hare haren ‘yan Boko Haram sannan ‘yan kungiyar IS reshen yammacin Afirka sunyi amfani da abubuwan fashewa sun kashe sojoji 5 masu sintiri.

Wani harin da aka kitsa a matsayin martini ya hallaka ‘yan ta’addan da suke da alhakin kai wadannan hare haren da dama, inji sojojin.

A hare haren baya bayan nan, maharan da suke karkashin wani sabon kungiyar tawaye ma suna Patriotic Movement for Freedom and Justice (MPLJ) a takaice sun yi ikirarin kai hari a wani sansanin soji dake wajen gari a yankin arewacin Agadez.

Sojin kasar sun bayyana cewa an kashe sojoji 2 sannan an jikkata wasu su 6 a harin da aka kai a ranar Talata.

Sojojin sun kara da cewa “ba tare da bata lokaci ba aka kaddamar da aikin gano maharan da suka arce wadanda suka nufi yankin kan iyakar Libya.

Kungiyar ta MPLJ tayi ikirarin kashe sojoji 14 da gurneti guda 2 a wannan harin, sannan an kashe ‘yan kungiyar su 2

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG