NIAMEY, NIGER - Wannan tsari an bullo da shi ne da nufin kawo karshen miyagun dabi’un da ke lalata hanyoyin zirga zirga.
Ganin yadda har yanzu direbobin motocin dakon kaya da ‘yan kasuwa dake odar kaya daga wannan jiha zuwa waccan ko kuma ma a tsakanin kasashe makwafta ke buris da dokar da ta kayyade lodin da ya wuce kima ya sa kwamitin da ke da alhakin fadakarwa kan maganar kare hanyoyin zirga-zirga kiran wannan taro domin tunatarwa akan abinda ake kira ka’ida ta 14 ta kungiyar UEMOA wace ta sami asali a shekarar 2005 kamar yadda magatakardan ofishin Ministan manyan ayyukan gine gine Alio Aminou ya shaida wa Muryar Amurka.
A washegarin bullo da tsarin kayyade lodin motocin dakon kaya gwamnatocin kasashen yankin na UEMOA sun kakkafa tashoshin sikeli a wurare da dama inda ake auna irin wadanan motoci sai dai matakin bai bayar da sakamakon da aka zata a can farko ba.
Loda kayan da yawansu ya zarta kima wani al’amari ne da ko baya ga lalacewar hanyoyi kan yi sanadin barnar dimbin dukiyoyi.
‘Yan kasuwa da masu motocin sufuri na tafka babbar asarar a dalilin haka inji Sakataren Kungiyar ‘yan kasuwar.
Gudunmuwar al’umma a yaki da miyagun dabi’un da ke lalata hanyoyin zirga-zirga wani abu ne da shugabanin al’umma suka ce na iya taimaka wa a magance matsalar cikin ruwan sanyi.
Mai martaba sarkin Konni Sardauna Mahaman Salissou na daga cikin Sarakunan da suka halarci wannan taro.
Dukan shugabanin sha’anin tsaro ne aka kira a wannan zama kasancewar jami’an tsaro na da alhakin sa ido kan motocin da ke kai da kawowa domin tabbatar da doka da oda.
Saurari cikakken rahoto Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna