Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kona Motocin Albasa: Barazana Ga Harkar Abinci Da Yarjejeniyar AfCFTA - Masu Ruwa Da Tsaki


Burkina Faso
Burkina Faso

Masu ruwa da tsaki, ciki har da masana harkar tattalin arziki da tsaro sun bukaci kungiyar ECOWAS da tarayyar Afrika ta AU su dauki matakin shawo kan rikicin Burkina Faso da ke zama babbar barazana ga samar da abinci a wasu kasashen yammacin Afrika da yarjejeniyar kasuwanci ta AfCFTA.

Wannan kiran na zuwa ne bayan da ‘yan ta'addan Burkina suka fadada hare-harensu zuwa kona motocin dakon albasa daga Nijar zuwa kasashen da ke makwabtaka da kasar kamar Ghana da Cote d’Ivoire, lamarin da ya sa wasu direbobin Ghana suka dakatar da zuwa Nijar domin dakon albasa.

Daya daga cikin direbobin da aka kona tirelolinsu da ya bukaci da a sakaya sunansa ya bayyana cewa dakon albasa daga Nijar zuwa Ghana a yanzu yana da hatsarin gaske.

"Sun kona motocinmu duka. In ka kuskura ka tsaya zasu harbe ka su kashe ka. Duk wanda ya san cewa yayi lodin kaya zuwa Nijar ya sauke kayan. Kuma wanda ya taso kada ya zo, saboda hanyar nada hatsari gaske"

Maharashtra, India, Dec. 19, 2018.
Maharashtra, India, Dec. 19, 2018.

Manyan motocin dakon albasa na ‘yan Ghana goma sha daya ne ‘yan ta'addan Burkina Faso suka banka wa wuta, abinda ya jefa direbobin cikin fargaba tare da neman hukumomi musamman na ECOWAS da su sanya baki a batun.

Usman Muhammad, shugaban direbobin da ke dakon albasa daga Nijar zuwa Ghana ya yi wa Muryar Amurka bayani.

"Sun tare motocinmu goma sha daya kuma suka konesu kurmus, bamu san abinda ke faruwa ba. Hakazalika ranar Talata sun sake tare motocinmu kuma suka kone kayan, a cewar Muhammad. Ya kara da cewa, in suka tare ku sai su karbi wayar direban su jefa a cikin motar su banka wa motar wuta. “Muna kira ga ECOWAS da su duba wannan lamari saboda kone-konen sun yi yawa," inji shi.

Wannan matsalar ta kone-konen motocin dakon albasa na barazana ga tsaron abinci a Ghana da kuma yarjejeniyar kasuwanci mara shinge tsakanin kasashen nahiyar Afrika wato AFCTA, inji Shu’aib Abubakar mai sharhi akan tattalin arzikin ciki da wajen Ghana.

Taron AfCTA
Taron AfCTA

Ya ce kasuwanci ba zai bunkasa ba a duk lokacin da ake tashin hankali. Ko wane irin kudi mutum ke nema in yana ganin zai iya rasa ransa idan ya tafi wani wuri to ba zai tafi ba. Kone-konen motocin na albasa ya sa wasu direbobi sun sauya hanya, yin hakan kuma zai sa su kashe kudi masu yawa wajen sayen mai.

Shuaib Abubakar na bukatar kasashen nahiyar su lalubo hanyar magance wannan rikici a Burkina Faso

Duk da cewa an dakatar da Burkina Faso cikin kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS sakamakon ci gaba da mulkin soja da ke gudana a kasar, Umar Sanda Ahmad, mai sharhi kan harkar tsaro na ganin kamata yayi ECOWAS ta girke dakaru domin kare al'umomin da ke tsallaka Burkina zuwa wasu kasashen da ke makwataka da ita.

ECOWAS
ECOWAS

"Lokaci ya kai da ECOWAS zata tura dakaru kamar yadda tayi a lokacin rikici a wasu kasashe kamar Cote d’ Ivoire da Liberia, don ganin an samu zaman lafiya a Burkina. Har idan kasashen da ke karkashin ECOWAS basu dauki mataki ba to abin zai wuce batun albasa ya fadada. Su kuma hukumomi a Burkina Faso ya kamata su dauki matakin gaggawa," inji Sanda.

A halin yanzu dai akasarin direbobin albasa sun dakatar da zuwa Nijar wasu kuma na bi ta Togo su shiga Accra.

Saurari rahoton Hamza Adam:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG