Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Sufuri Sun Fara Dakatar Da Jigila Daga Nijar Zuwa Burkina Faso Saboda Matsalar Tsaro


Sojojin Tafkin Chadi-Nijar
Sojojin Tafkin Chadi-Nijar

Yanayin tsaron da aka shiga akan iyakar Burkina Faso da jamhuriyar Nijar ya sa wasu kamfanonin jigila dakatar da zirga-zirga tsakanin birnin Yamai da Ouagadougou da nufin kaucewa fadawa tarkon ‘yan bindiga da suka addabi wannan yanki.

NIAMEY, NIGER - Lura da munanan hare-haren da aka fuskanta a tsawon kwanaki da dama jere da juna a garin Seytenga na kasar Burkina Faso da harin da yayi sanadiyar mutuwar jandarmomi a garin Waraou, ya sa kamfanonin jigila suka fara dari-darin bin hanyoyin dake tsakanin wadanan kasashe biyu don gudun jefa fasinjoji cikin hadari.

A bayan nan kamfanin jigila na SONITRAV ne ya bada sanarwar dakatar da aiki a tsakanin biranen Yamai da Ouagadougou, ratsawa ta garuruwan Tera da Dori.

Mataimakin babban darektan kamfanin Mohamed Khamed yayi bayani akan dalilan daukan wannan mataki, na kare jama’a.

Koda yake hukumomin Nijar sun shimfida tsarin da a karkashinsa jami’an tsaro ke yiwa matafiya rakiya tun daga gundumar Tera har zuwa iyakar kasar da Burkina Faso, masu motocin jigila na ganin dakatar da aiki itace hanya mafi a’ala har zuwa lokacin da al’amura zasu lafa.

Mun yi katarin haduwa da wani dreban bus Sawadogo Abdoulaye ‘dan kasar Burkina faso da ya shigo birnin Yamai a jiya alhamis dauke da lodin fasinja daga Ouagadougou.

Ya ce sun ce motarsu ba za ta iya zuwa Yamai ba daga Ouagadougou saboda haka ya amince da tayin kwashe fasinjojin da ya kamata su dauko saboda yadda direbobi kan taimaka wa juna idan bukata ta taso.

Ya kara da cewa bayan ya isa ne ya samu labarin matsalar tsaron da ake fuskanta da ta sa suka dakatar da aiki. Kuma akan hanya ya lura da tarin mutane dauke da kaya suna tafiya a kasa, kuma da suka ratsa garin Seytenga mutane sun watse, daga nan ne ya samu labarin an kai hari a garin. Ya ce bai taba zuwa birin Yamai ba, shine karon farko da ya bi wannan hanya.

Tabarbarewar al’amuran tsaro a tsakanin Burkina Faso da Nijar ta kai matsayin da mutanen da tafiya ta zame wa dole kan yi dogon kewaye zuwa kasar Togo kafin su shiga Ouagadougou ko kuma su je birnin Yamai, yayin da wasu kuma ke daukar kasada saboda rashin wata madogara.

A watannin baya ‘yan bindiga sun kona wata motar jigilar kamfanin STM tare da karkashe fasinjoji da dama lamarin da ya sa kamfanin dakatar da aiki a kan wannan hanya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Kamfanonin Suhuri Sun Fara Dakatar Da Aiki Akan Hanyoyin Nijar Da Burkina Faso Don Gudun ‘Yan Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG