Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Dauki Sabon Mataki Wajan Kwato Tungar Mayakan ISIL


Ministocin tsaro daga kasashe sama 30 sun amince da matakin gaba da za a ‘dauka na kwato tungar mayakan kungiyar ISIL ta karshe.

Biyo bayan taron da akayi a wani sansanin sojan Amurka dake wajen Washington, sakataren tsaron Amurka Ash Carter yace, matakin kungiyar hadin gwiwar na gaba shi ne shiga da ikon birnin Mosul, wanda yake tungar ‘yan kungiyar ISIS a Iraqi da Raqqah dake Siriya.

Jami’ai dai sunce Carter yayi amfani da taron na jiya Laraba, wajen samun dabarun yadda za a kawo karshen mayakan a Iraqi da Siriya, musammam ma yanzu da Iraqi ke shirin shiga ta kwato birnin Mosul, babban birnin kasar dake karkashin ikon ‘yan ta’addar.

A makon da ya gabata Amurka ta yi alkawarin barin karin sojojinta 560 domin taimakawa kokarin da ake na kwato Mosul. Bayan taron ne Carter ya bayyana cewa sauran kasashe da halarci taron sunyi aniyar bayar da tasu gudunmawar don tabbatar da cewa an sami nasara akan yakin da ake da kungiyar ISIS.

XS
SM
MD
LG