Haka an bada rahoton dakatar da alkalai kusan 2,745 bisa zargin alaka da wani Malamin addini Fetullah Gulen. Kafar yada labaran Turkiyya tace an mika sammaci 140 ga wasu ma’aikatan babbar kotun kasar.
Malamin da aka zarga da hannu a wannan yunkuri Fetullah, wanda yake zaune a jihar Pennsylvania ta nan Amurka, ya nisanta kansa da yunkurin juyin mulkin.
Sakataren harkokin wajen Amurka yace, Turkiyya bata bukace su da mika Shehin Malamin ba, to amma Amurka a shirye take ta mika shi matukar aka sami kwararan hujjojin cewa yana da hannu a yunkurin juyin mulkin da ya kasa kaiwa ga gaci.
Har yanzu dai ba wanda ke da yakinin ko suwa ke rike da ikon shelkwatar sojin kasar ta Turkiyya. Firayimistan kasar Binali Yildrim ya yiwa jama’a jawabi a yau Asabar game da yunkiurin juyin mulkin da aka yi, yace, wannan bakin tabo ga kasarsu.