Manema labarai a kasar ta Turkiyya sun ce sun ga jiragen sojoji suna ta shawagi a babban birnin kasar kana sojoji sun rufe wata gada da ta ratsa ta kan mashigin ruwan Bosphorus.
Koda ya ke, Firai Minista Yildimir ya ce, zai zama kuskure idan aka kira lamarin a matsayin juyin mulki, amma kuma akwai yunkurin da wani bangaren sojin kasar ke yi na karbe mulkin kasar.
"Wasu mutane sun dauki doka a hannunsu ta hanyar tsallake magabatansu a dakaru kasar." In ji Yildimir, yayin da ya ke wani jawabi a gidan talbijin na NTV.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters shima ya ruwaito wannan lamari.
Firai Ministan ya kara da cewa "gwamnatin da mutane suka zaba har yanzu ita ce akan karagar mulki, wannan gwamnati za ta sauka ne kadai idan mutane suka bukaci ta yi hakan."
Yildimir ya kuma nanata cewa, ba za su taba bari a katse mulkin dimokradiyya ba, ya kuma sha alwashin cewa za a hukunta wadanda ke da hanu a wannan yunkuri.