Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kaiwa 'Yan Sanda Sabon Harin Da Ya Kashe Uku a Jihar Louisiana Ta Amurka


'Yan Sanda Sun Tare Hanya Bayan Harbin Wasu a Garin Baton Rouge, Louisiana, July 17, 2016.
'Yan Sanda Sun Tare Hanya Bayan Harbin Wasu a Garin Baton Rouge, Louisiana, July 17, 2016.

An kaiwa 'yan sanda sabon hari an kashe uku an jikkata uku a jihar Lousiana ta nan Amurka, tare da kashe daya daga maharan.

A kalla a yau Lahadin nan an harbe wasu ‘yan sanda guda uku har lahira tare da jikkata wasu guda ukun ya zuwa yanzu da aka sami wannan rahoton daga garin Baton Rouge da ke jihar Louisiana ta Amurka, kamar yadda hukumomin jihar suka bayyana.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin ya bayyana cewa an kashe mutum daya a cikin wadanda ake zargi da kai harin a wajen, sannan guda biyu sun tsere ana nemansu ruwa a jallo.

Shima Gwamnan Jihar ta Louisiana John Bel Edwards ya kira harin kisan gillar a matsayin wani abin takaicin da ba ma a magana bisa tsagwaron yadda aka aikata wannan rashin adalcin kisa.

Yace musamman ma a daidai wannan lokacin da ba’a gama jimamin kisan gillar da wani dan sanda yayi wa wani bakar fata Alton Starling ba, wanda aka yayata a kafar sadarwar intanet da hakan ya haddasa bore a wurare da dama.

Sakamakon haka ne a zanga-zangar da aka yi a Dallas, wani bakar fatar ya bindige ‘yan Sanda biyar a garin da ke jihar Texas. Daga karshe Gwamnan ya bada tabbacin da sannu wadanda suka aikata laifin nan zazu shiga hannu don fuskantar hukuncin laifinsu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG