Wannan na’urar dai ana amfani da ita ne wajen gano jiragen ruwan soji na karkashin teku.
To amma kotun tarayyar tace, amfani da Sonar din zai iya cutar da halittun da ke rayuwa a cikin teku, wanda suka hada da kamar manyan kifayen Shak da kuma Wels da sauran halittu makamantansu.
Sannan ko ba komai, nau’rar zata dama musu lissafin yadda namun ruwan ke farautar abincinsu da kuma yanayin hayayyafar da suke yi a karkashin teku. Dokar da aka yanke a shekarar 2012.
Wacce hukumar kula da kan teku da ayyukan lura da kifaye suka runguma, bisa sharadin duk lokacin da sojojin ruwan ke amfani da na’urar.
Hakan na nufin da zarar sun hangi dabbobin ruwan a kusa da inda jirgin ruwansu na soja yake, har sai dabbobin ruwan sun bar wajen kafin su ci gaba da aiki da ita.