Kasar Jamus ta ce ‘yan kasarta uku ne suka rasu yayin da ita Algeria ta bayyana mutuwar mutane uku.
Ita kuwa Morocco ta bayyana mutuwar mutanenta biyu ne kana Armenia da Switzerland suma suka ce ‘yan kasar kasashenta biyu ne suka mutu.
Sannan a daya bangaren kuma Rasha da Ukraine mutum guda -guda
Hukumomin Faransa sun ce sunan mutumin da ya kai harin Nice da ya halaka mutane 84, Mohamed Lahouaij Bouhlel.
Bouhlel ya tuka wata babbar mota ce ya abka kan mutanen da suka taru domin bikin zagayowar ranar da aka yi juyin juya hali a Faransa da ake yiwa lakabi da ranar Bastille.
Daga cikin wadanda suka mutu har da kananan yara goma, sannan ‘yan sanda da yawa ma sun mutu, yayin da wasu 18 da suka tsira ke cikin wani mawuyacin hali a asibiti., wato daga cikin mutane 50 da suka jikkata.
Maharin dai ya tuka motar a cikin dandazon mutanen na tsawon kilomita biyu kuma bai tsaya ba har sai da ‘yan sanda suka harbe shi har lahira.
Bouhlel dan asalin kasar Tunisia ne amma haifaffen Faransa mai shekaru 31 wanda ke zaune a birnin na Nice.
‘Yan sanda Faransa sun ce sun san maharin domin an taba samunsa da kananan laifuka kamar na mallakar kwaya, amma ba su taba tunanin ya na da alaka da wata kungiyar ‘yan ta’adda ba.
Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya ce babu tantama, wannan hari ne na ta’addanci.
“Babu wani abu da zai sa mu ja da baya a yakin da mu ke yi da ta’addanci.” In ji Hollande, yayin da ya yiwa ‘yan kasar wani jawabi a yau Juma’a.
Obama Ya Yi Allah Wadai Da Harin
Shugaban Amurka Barck Obama, ya yi tir da mummunan harin da aka kai na Faransa, inda ya umurci jami’an kasar da su baiwa Faransan duk irin taimakon da ta ke bukata.
“A wannan rana, an tuna mana da irin jarumtakar da Faransa ke nunawa da jajircewarta akan dimokradiya, wanda hakan ya sa ta karbu a duk fadin duniya, kuma mun san cewa kasar za ta sake farfadowa bayan wannan hari." Obama ya ce.
Ita kuwa Hillary Clinton da ake tunanin ita za ta tsayawa jam’iyar ta Democrat takara a zaben shugaban kasa cewa ta yi harin ya sa ta ji ba dadi a zuciyarta yayin da abokin hamayyarta Donald Trump ya kwatanta harin a matsayin wani "babban mummunan abu," inda ya ce zai dage shirinsa na bayyana abokin takararsa a yau Juma’a, koda ya ke daga baya bayyana daga baya a shafinsa na Twitter.
Yadda Wurin Harin Ya Kasance
Da zaran mutum ya ga babbar motar da aka kai harin da ita, zai lura cewa gilashin motar ya na dauke da huji-huji, wanda ake tunani daga harbin bindigogin ‘yan sanda ne.
Wasu da suka shaida lamarin sun ce maharin ya bude wuta da bindiga kafin daga bisani ya tuka motar cikin jama’a da ke gefen titi.
Nan da nan aka mayar da dakin karbar bakin wani otel da ke kusa wajen ba da taimakon gaggawa, sannan aka umurci kowane asibiti ya zauna cikin shirin karbar wadanda suka jikkata tare da firgita daga harin.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, matukin motar ya bige wani shingen da aka dasa a gefen hanya, sannan daga baya ya yi ta tattake mutane da ke tafiya a gefen hanya.
Jami’an tsaro sun ce an samu motar shake da ababan fashewa da gurneti-gurneti da kuma wasu makamai.
Wannan hari shi ne na uku tun bayan shekarar da gabata, inda aka kai wasu jerin hare-hare a Paris da suka halaka mutane 130, harin da kungiyar IS ta dauki alhaki, sannan an kai wasu jerin hare-hare akan ofishin mujallar barkwancin nan ta Charlie Hebdo inda mutane 17 suka mutu.