Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yola Babban Birnin Jihar Adamawa Ya Cika Ya Batse da 'Yan Gudun Hijira


Wasu mata 'yan gudun hijira.
Wasu mata 'yan gudun hijira.

Wakilin Muryar Amurka ya yi tattaki zuwa sansanin 'yan gudun hijira dake Yola wadanda da suna gudun hijira a Gwoza, Gulak, Michika,Madagali da Mubi amma suka sake gudu zuwa Yolan domin kame wuraren da suke da 'yan Boko Hara suka yi.

Kidigdiga ya nuna cewa kawo yanzu kimanin mutane dubu dari shida da hamsin suka rasa muhallansu ko kuma suka kaurace masu sabili da yadda 'yan Boko Haram suke kame wurare suna kashe na kashewa da sace na sacewa.

A birnin Yola dubban 'yan gudun hijira ne suka cika garin. Wasu suna kan gudun hijirarsu sau uku ko hudu ke nan sabili da kame inda a da sun sami mafaka. Akwai wadanda kawo yanzu Yola ne gari na hudu da suka nemi mafaka. Cikin 'yan gudun hijiran har wadanda suka gudo daga Gwoza da Bama duk a jihar Borno.

Mutanen da aka zanta dasu sun ce lamarin ya fi karfinsu domin fiye da wata daya ke nan suna kan gudu. Duk da yawansu ana basu abinci suna ci yara kuma da suka kamu da ciwo ana kula dasu.

Mata da yara su ne abun ya fi shafa. Akwai wadanda aka kashe ma 'yan uwa da mazajensu. Wasu mazan an kamasu ne a dakunansu. An harbe wasu kana kuma wasu an yi masu yankan rago. Mayakan sun zolayi matan inda suka ce kada su damu zasu kula dasu amma daga bisa ni sai suka soma sacesu lamarin da ya sa wasu da suke da sauran kwana suka yi ta kare. Mata ne suka yi jana'izar mazajensu domin babu sauran maza da zasu yi masu.

Kungiyoyi da shugabannin al'umma da 'yan siyasa da hukuma dake bada agajin gaggawa suna taimaka masu. Ita hukumar bada agajin gaggawa take sa ido a harkokin 'yan gudun hijiran tana yi masu ragjista.

Malam Saidu Alkali jami'in hukumar bada agajin gaggawa na kasa yace suna yiwa mutanen ragista a duk inda suka tsugunar dasu. Kullum mutane sai kwararowa suke yi.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG