Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kiran Shugaba Jonathan Ya Tasa Keyar Kwamitin Tallafawa Tagayyaru Maiduguri


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Cibiyar kare hakin bil Adama da tallafawa jama'a ta kira shugaba Jonathan ya tasa keyar kwamitin da ya kafa domin tallafawa jama'ar da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu a jihohin Adamawa, Borno da Yobe da ma wasu wurare.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa yana karkashin shugabancin Janaral T.Y. Danjuma ne da manufar tara kudi domin tallafawa jama'a da suka tagayyara sanadiyar rikicin Boko Haram.

Kawo yanzu an samu watanni biyu da aka kafa gidauniyar a karkashin kamitin wadda shugaban kasa ya kafa a babban birnin tarayyar Najeriya wato Abuja. Ranar da aka kafa gidauniyar aka bayar da sanarwar an tara zunzurutun kudade nera miliyan dubu sittin da biyar domin tallafawa wadanda rikice rikicen Boko Haram ya daidaita musamman na jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da ma wasu yankunan da rikicin ya shafa.

San'ina Buba shugaban cibiyar yace sun zo Abuja ne su sanarda gwamnatin tarayya cewa rigingimun sun isa. Ya kamata a kara karfi da karfe a ciwo kan lamarin ba tare da banbancin siyasa ba ko na kabila ko na addini. Abun da ya dameshi ana sa siyasa cikin lamarin. Abun da ya kara bashi mamaki, shi ne, su ana kashesu a Maiduguri kwamitin tallafi kuma yana nan a Abuja.

Kullum aka tayar da maganar sai a ce suna mitin. Yawancin mutane da ake sawa cikin kwamitin bada tallafi mutane ne da basa zaune inda rikicin ke faruwa kamar Maiduguri. Buba ya roki shugaban kasa ya tasa keyar kwamitin Janaral Danjuma Maiduguri domin tun da aka kafa kwamitin bai je Maiduguri ba.

An tara zunzurutun kudade amma mutane na mutuwa. Mutane basu da wurin kwana ba isasshen abinci. Mata da yara suna kan layin neman abun sawa a baka.

Akan jihar Borno yace gwamnan yana bada kudi. Ya sha bada nera miliyan dari dari duk ana ba Galtimari ya raba tamkar babu wasu mutane ne a jihar da za'a iya anfani dasu. Yace yakamata gwamna ya sauko kasa ya duba. Idan ya ba talakoki kudaden zasu kai inda ake bukatarsu. Akwai masu kishin jihar da dama. Abun da gwamnati ke bayarwa baya isa hannun mutane.

Kwamitin da aka kafa akan Bama maganar ta mutu. Na gidan kwastan shi ma ya mutu. Sun sha fadawa gwamna amma baya jinsu. Sabili da haka sun kai inda zasu fito waje su fadi gaskiya.

To saidai Buba yace ya gode domin yanzu ana ba mutanen da suke sansanin gudun hijira abinci sau uku rana.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG