Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram ta Shiga Sace Mata da Matasa


Wasu da suka tsere daga hare haren 'yan Boko Haram.
Wasu da suka tsere daga hare haren 'yan Boko Haram.

Rahotanni na cewa mayakan Boko Haram dake rike da wasu sassan jihar Adamawa sun canza salo inda suka shiga sace mata da matasa masu jini a jika.

Wasu da suka samu suka tsere daga Madagali daya daga cikin yankunan dake hannun 'yan Boko Haram din sun shaida cewa yanzu 'yan kungiyar suna sace mata da maza matasa.

A garin Gulak hekwatar karamar hukumar Madagali 'yan Boko Haram sun sace mata da matasa su kimanin hamsin a hare-haren da suka kai a wasu kauyuka dake yankin. Mayakan sun bi gida gida suna kwasan yara da mata da matasa yayin da suke fadawa mutane kada su damu fadansu da azzalumai ne, wato sojoji da 'yansanda da jami'an gwamnati.

Shugaban karamar hukumar James Watanda ya tabbatar da lamarin wanda yace al'ummarsa na cikin mawuyacin hali sabili da kame-kamen da 'yan Boko Haram suke yi.

Akwai labarin dake cewa a fara tura sojoji yankin amma basu fara shiga garin Gulak ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG