Kungiyoyi da daidaikun ‘yan Nijeriya na cigaba da kiraye-kirayen gwamnatin Nijeriya ta dau mataki kan mutanen da Baturen Australia Stephen Davis y ace sun a taimakawa ma Boko Haram.
Alhaji Ibrahim Garba Wala ya ce kamar yadda Baturen na kasar Australia ya taimaka da bayani, su ma a matsayinsu na ‘yan Nijeriya za su taimaka wajen ankarar da gwamnatin Nijeriya muhimmancin binciken wadanda aka zarga din. Y ace binciken shi zai nuna ko sun aikata ko kuma a’a; zai kuma nuna ko da Karin wasu da ke taimakawa ‘yan Boko Haram din ko a’a.
Shi ko Baballe Sarkin Hausawan Kuma kuma Shugaban Kungiyar Rundunar Adalci ta Gombe y ace kamata ya yi a rinka gaya ma Shugaban kasa gaskiya a irin halin da ake cikin a maimakon labaran siyasa.
Shi ma a nasa ra’ayin, sanannen lauyan nan mai tsokaci kan al’amuran zamantakewa da siyasa, Barrister Solomon Darlong, yace daga kuduncin Nijeriya ne aka kirkiro kungiyar Boko Haram aka cinna ma arewa don a kassara ta. Y ace an yi ta samun ‘yan kudancin Nijeriya da hannu a hare-haren da aka yi ta kaiwa da sunan Boko Haram. Don haka y ace an fara Boko Haram ne da sunan addini amma daga baya sai ya rikide ya zama na siyasa.