Muhammed Alhaji Hassan shugaban kungiyar cigaban garin Baya shi ya bayyanawa Muryar Amurka cewa har yanzu fa garin nasu yana hannun 'yan kungiyar Boko Haram tun da suka kamashi kwanaki goma sha daya da suka wuce.
Suna kiran gwamnatocin jiha da na tarayya cewa har yanzu garinsu na hannun 'yan Bokjo Haram da rashin sanin makomar iyalansu da suka bari baya. Kawo lokacin da yake bada labari babu wani sojan Najeriay da yake cikin garin.
Dangane da yadda Alhaji Hassan ya san cewa babu sojoji a garin sai yace wani daga cikinsu ya shiga kogi ya tsallake zuwa wani gefe inda ya samu ya gudo cikin gajeren wando. Babu wani tabbas akan irin halin da mutanen ke ciki.
Yawancin 'yan Baman suna sanssanonin 'yan gudun hijira cikin garin Maiduguri kana kuma akwai wasu da dama cikin gidajen mutane.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.