Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Karin Gawarwakin 'Yan Boko Haram A Dajin Konduga


Gawarwakin mutane bayan wani harin da aka kai Konduga kwanan baya.
Gawarwakin mutane bayan wani harin da aka kai Konduga kwanan baya.

Bayan farmakin da sojojin Nijeriya su ka kai garin Konduga su ka karkashe 'yan Boko Haram da yawa, an cigaba da samun gawarwakin 'yan kunghiyar a daji, baya ga wadanda su ka yi ta gudowa zuwa cikin gari.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Maiduguri y ace ga dukkan alamu jita-jitar da aka yi ta yadawa cewa ‘yan Kungiyar Boko Haram na gab da shigowa cikin birnin Maiduguri ba gaskiya ba ne. Y ace amma jita-jitar ba za ta rasa nasaba da hare-haren da kungiyar ke kai wa a garuruwan kewaye ba.

Wakilin namu, Haruna Dauda Biu ya gaya ma Halima DJimrao ta wayar tarho cewa gaskiya ne sojojin Nijeriya sun yi nasara kan ‘yan Boko Haram a samamen baya-bayan nan da su ka kai kan kungiyar a yankin Konduga. Ya ce an ma yi ta samun Karin gawarwakin ‘yan kungiyar a daji. Saboda haka, in ji shi, a yanzu adadin ‘yan kungiyar da aka kashe a yankin na Konduga zai haura 100.

Haruna y ace ya ma ga wani dan Boko Haram din da ya gudo ya shigo cikin birnin Maiduguri saboda tsananin zafin yakin da aka tafka a yankin na Konduga. Ya ce su wajen 10 ne su ka shigo birnin na Maiduguri saboda tsananin yakin da aka yi a dajin na Konduga. Haruna ya ce ya ga ‘yan Kato Da Gora na ta masa tambayoyi shi kuma ya na amsawa, ya na ba su hadin kai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG