Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Mutane A Najeriya Ya Kai Miliyan 216 A 2022 - Majalisar Dinkin Duniya


Mutanen Najeriya
Mutanen Najeriya

Sashen tattalin arziki da zamantakewa na Majalisar Dinkin duniya ya fitar da wani rahoto dake nuna cewa yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 216 a shekarar 2022, da hakan ya kai kashi 2.7 na al’ummar duniya.

BORNO, NIGERIA - Hakan na nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashe takwas da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Masar, Habasha, Indiya, Pakistan, Philipines da Tanzaniya dake bada gudumawa wajen saurin karuwar yawan mutane a duniya.

A duk lokacin da mutum ya shiga cibiyoyin lafiya matakin farko ko asibitocin haihuwa zai ga dafifin mata masu juna biyu a Najeriya ko kuma wadanda su ka kawo jariran su rigakafi.

Wani yaro ana yi mashi allurar rigakafi
Wani yaro ana yi mashi allurar rigakafi

Dr. Adama Ibrahim Jibril da ke aiki a asibitin mata da yara a Jihar Kano ta ce matan na fahimtar muhimmancin bayanan tazarar haihuwa da kula da yara ko da kuwa ba dukan su ke samun nasarar aiwatar da shawarwarin da aka ba su ba.

Hukumar yawan jama’a ta Najeriya da ke shirin kidaya a Afrilun badi ta tabbatar da ingancin rahoton na Majalisar Dinkin Duniya.

Dr. Ahmad Sagir na asibitin koyarwa da ke Gwagwalada ya ce likitoci da jami’an kula da lafiya na kokarin wayar da kan jama’a wajen muhimmancin tazarar haihuwa don taimakon lafiyar jarirai da uwayen su.

Kungiyoyin kula da hakkokin kananan yara na kokawa kan yadda mutane kan haifi yara ba tare da kula da su ba ta hanyar barin su suna gararamba kan tituna.

Sa’idu Sambo Kaftan da ke da kungiyar raya ilimin yara a Arewa, ya ce su kan samu yara da yawa da iyayen su suka fita sha’anin su musamman don talauci ko halin ko in kula.

Alkaluma sun nuna zuwa shekara ta 2050 adadin mutanen duniya zai karu daga mutum biliyan 8 zuwa biliyan 9.75.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar cikin sauti:

Yawan Mutane A Najeriya Ya Kai Miliyan 216 A Shekarar 2022 - Majalisar Dinkin Duniya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:08:05 0:00

XS
SM
MD
LG