Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamfara Ta Musanta Kididdigar Da Ta Dora Ta A Ma'aunin Jihar Da Ta Fi Matalauta A Najeriya


Gwamnan Zamfara Bello Matawalle.(Facebook/Zamfara Dep Governor)
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle.(Facebook/Zamfara Dep Governor)

Hukumomi a Zamfara sun mayar da martani dangane da wani rahoto da ya dora jihar a wani mizanin da ya nuna ita ce ta fi kowacce jihar matsalar talauci a daukacin Najeriya.

Hukumar da ke yin rijista ta Najeriya mai suna ‘National Social Register’ (NSR), ce ta fitar da alkaluman, wadanda suka nuna mafi aksarin al’umar jihar wacce ke arewa maso yammacin kasar na zaune cikin talauci.

Kwamishiniyar Maaikatar Harkokin Jin Kai ta jihar Zamfara, Hajiya Faika Marshel, wacce batun talauci ke karkashin Ma’aikatarta, ta ce ko kadan ba gaskiya ba ne.

Ta ce wadanda suka yada labarin, sun yi amfani ne da sakamakon rahoton shekara ta 2019, wanda jihar Zamfara ta zo matsayi na karshe lokacin da ta samu Kashi 91.8 bisa 100 a ma’aunin talauci a jerin jihohin da suka fi talauci a Najeriya.

“Gaskiya wannan hasashen da aka yi, kwata-kwata ba kan ka’ida yake ba, saboda ita wannan NSR, ana maganarta ne akan iya inda aikinta ya kai. Aikinta ya a bisa ka’ida kamar yadda aka shirya, ya kamata za ta karade kasar nan baki daya ne. Kaga yanzu a jihar Zamfara, aikin nan ya kai kashi 95 bisa 100. Kamata ya yi a godewa jihar Zamfara saboda ta daga tuta.” In ji Kwamishinyar ayyukan jin-kai ta jihar Zamfara Faika Marshall.

Ta kara da cewa, wasu jihohin kashi uku ka wai suka iya yi zuwa yanzu, saboda haka kuskure ne a yanke hukunci alhali Hukumar rijistar ta Najeriya ba ta kammala aikinta a kasa baki daya ba tana mai cewa, kashi 17.5% ta samu yi yanzu wanda ya zo daidai da iyalai miliyan talatin da biyar da dubu dari biyu da sittin da biyar da casa'in (35,265,096).

Karin bayani akan: jihar Zamfara, NSR, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“A kasar nan, akwai jihar da kashi 3 kadai ta samu ta yi na wannan aiki, babu hurumin da za a ce an danganta wasu da ma’aunin talauci, tun da abin da kasa gabaki daya ta yi record na wannan aiki, miliyan 35 da dari biyu da sittin da bakwai da casa’in da shida.” Ta kara da cewa.

Faika Marshel ta kara da cewa a yayin da Zamfara to karade mazabu 140 wajan kididdiga, mazabu 7 suka rage, ta kuma raba tiraloli 170 dauke da abinci ga al'umar jihar da ke kananan hukumomin 14 a Jihar.

“Idan aka mayar da shi a ma’aunin kashi, shi ne za ka samu 17.5 a cikin kashi 100. Amma idan ka dauki jihar Zamfara ita kadai, ta yi Kashi 95 a cikin 100. To ka ga a jihar Zamfara, ta gama da ward 140, ward bakwai ya rage mata a gama, wanda yake a fadin Najeriya, yanzu akwai wasu kashi uku suka yi.”

Faika Marshall, wacce ta yi waiwaye, ta kara da cewa, a shekarar 2019, gabanin su kama aiki, Zamfara an kiyasta cewa ita ce ta karshe a fadin Najeriya, saboda an ce ma’aunin talauci ya nuna tana matsayin kashi 91.8.

Ta kara da cewa a yanzu al’amura sun inganta a Zamfara inda take da kashi 73.84% a ma 'aunin talauci.

“Amma a yanzu, mun koma kashi 73.84….. ita NSR bawai sun yi kuskure ba ne, amma kuskuren da aka samu shi ne, a ce za a auna talauci akan maganar rijista ta ‘social register’ dalilin kenan da ya sa muka fito muka yi wannan gyara, domin mutane su sani.”

Saurari cikakken rahoton Sani Shu'aibu Malumfashi:

Zamfara Ta Musanta Kididdigar Da Ta Dora Ta A Ma'aunin Jihar Da Ta Fi Matalauta A Najeriya - 3'06"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


XS
SM
MD
LG