Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Kunar Bakin Wake a Harabar Kano Poly da Bom


 Bom ya fashe a harabar makarata a Kano.
Bom ya fashe a harabar makarata a Kano.

Wata ‘yar kunar bakin wake ta kai hari harabar kwalejin fasaha ta Kano.

Wata ‘yar kunar bakin wake ta kai hari harabar Ofishin harkokin gudanarwa na kwalejin fasaha ta Kano wato Kano Polytechnic, ta hallaka kanta kuma ta kashe mutum uku.

Lamarin ya afkune bayan da ‘yan kunar bakin waken ta shiga cikin daliban dake duba sunayen su a allon da aka kafe jerin sunayen daliban da suka kammala karatu kuma zasu tafi aikin yiwa kasa hidima, wato NYSC.

Dr. Dalhatu Galadanchi, shine shugaban kwalejin fasahar ta Kano, yace “ wani abune ya fashe bamusan ko menene ba, wata yariya ta rasu kuma kimanin mutun hudu an daukesu zuwa asibiti, abun da muka sani kennan yanzu dai ga jami’an tsaro suna aikin su.”

Ya musata cewa an kai harin ne saboda sunayen da aka kafe na masu yiwa kasa hidima.

Wannan aika-aika bata da alaka da sunayen da aka kafe na masu tafiya yiwa kasa hidima inji Dr. Galadanchi.

Kwamishina ‘yan sandan jihar ta Kano Mr. Aderele Shinaba, ya umarci jama’a da su kara bude idanu dangane da abubuwan dake faruwa a zagayen mu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG