Hare-haren da aka kai a Garkida dake karamar hukumar Gombi sojoji hudu ne suka halaka amma har yanzu ba'a tantance adadin fararen hula da 'yanbindigan suka kashe ba.
Yayin da yake karbar sarakunan jihar da suka ziyarceshi, mukaddashin gwamnan Ahmed Umaru Fintiri ya bukaci al'ummar jihar da su dukufa da yin addu'o'i na neman Allah Ya kawo karshen bala'in da ya addabi jihar da kasar gaba daya. Ya ambato lamarin da ya faru a Garkida inda ya yiwa wadanda suka rasa 'yanuwa ta'aziya. Yace zasu cigaba da yin addu'a Allah Ya sa su san yadda zasu yi adalci su rabu da gwamnati lafiya. Zasu yi duk abun da zai sa a zauna lafiya a jihar.
Bayan sun yi addu'o'i sarakunan sun bayyana irin matsalolin da al'ummominsu suka samu kansu a ciki. Sarkin Ganye Alhaji Umaru Adamu Sanda da kuma Hamma Bachama Alhamdu Gladstone suka koka cewa akwai wahala wurin yin tafiya a hanyoyin yankunansu. Sun ce kodayaushe zasu kawo kuka idan an samu dama a taimakesu. A yiwa gwamnatin tarayya magana ta share masu hawaye.
Shugaban majalisar sarakunan Adamawa Lamidon Adamawa Dr Muhammed Aliyu Mustapha ya shawarci mukaddashin gwamnan da ya taka sannu-sannu domin ya ciyar da jihar gaba. Yace Allah ne Ya bashi kuma kullum ya tuna da maganar Allah, ya bi umurnin Allah domin Ya fi kusa dashi. Duk abun da mukaddashin gwamnan yayi Allah yana nan.
An kammala taron ne da addu'o'in da shugabannin addini suka gabatar bisa ga irin halin da jihar ke ciki.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.