Jiya Lahadi aka yi sallar idi a unguwar Sasa dake garin Ibadan. Sallar ita ce alamar kammala karshen azumin wannan shekarar da aka yi kwana ashirin da tara ana yi.
Uztaz Mumahhed Usman shi ne ya jagoranci sallar idin inda ya yi huduba bayan an kammala sallar.
Da yake amsa tambaya akan abun da hudubarsa ta kumsa Uztaz Muhammed Usman yace abu mafi mahimmanci shi ne tabbatar da adalci akan zamantakewar jama'a. Kowane mai haki a bashi hakinsa. Yin hakan kawai zai tabbatar da zaman lafiya da albarkar Ubangiji. Allah ba azzalumi ba ne. Kuma Yayi rantsuwa da zatinsa cewa idan bawansa yayi kara yace sai Ya sakawa bawan. Zaman adalci tsakanin jama'a ke kawo zaman lafiya. Zalunci na ruguzar da tattalin arzikin kasa. Zalunci na rugutar da zamantakewar al'umma.
Dangane da tashe-tashen hankula dake faruwa musamman a arewacin kasar Uztaz Muhammed yace mataki na farko da ya kamata a dauka akan abubuwan dake faruwa shi ne a ji tsoron Allah daga sama har kasa. Kowa ya gyara tsakaninsa da Allah. Kowa ya ba danuwansa hakinsa daga gwamnati zuwa al'umma da sauransu, tsakanin mahukunta da talakawa da tsakanin Kirista da Musulmi. A ba kowa hakinsa.
Wasu sun bayyana yadda suka yi bukuwan sallar. Sun yiwa Allah godiya da Ya sa suka kammala azumi lafiya kuma suka ga ranar sallah. An kira masu hannu da shuni su dinga taimakawa wadanda basu dashi. A taimakawa wadanda basu da karfi.
Sarkin Sasa Haruna Mai Yasin Katsina ya kira 'yan Najeriya da a zauna lafiya. A cigaba da addu'o'i domin kawar da kowace irin masifa.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.