Mai martaban yayi kiran ne a fadarsa lokacin da yake taya mutane murnar ganin sallah ta karshen azumi.
Shehun Borno yace babu yadda za'a samu cigaba a kowace kasa ba tare da samun zaman lafiya ba. Yace daruruwan mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon rigingimun da suke faruwa. Bayan ya kammala jawabinsa sai babban sakataren fadar Alhaji Zanna Lesu ya kara haske cikin harshen Hausa.
Yace sakon Shehun ga mutane shi ne su cigaba da yin addu'a domin irin halin da aka shiga musamman jihohin Borno da Adamawa da Yobe da sauran sassan kasar. Yace ga masifar kashe-kashe da kuma tashin tashinar 'yan kungiyar Boko Haram. Ya bada tabbaci Allah zai kawo sauki.
Bana ba'a yi hawan sallah ba domin irin yanayin da jihar ke ciki. Misali a Borno akwai mutane da yawa da suka rasa muhallansu daga kauyuka suka shigo Maiduguri. Ban da haka akwai kashe-kashen mutane da ake yi a cikin gari. Hatta wasu sarakuna sun rasa rayukansu. Sabili da wannan yanayin Shehun yace bai kamata a tashi ana yin hawan daba ko wasu bukukuwa ba. Maimakon hakan a cigaba da addu'o'i saboda kasa ta samu zaman lafiya.
Wasu kungiyoyi sun ziyarci fadar Shehun cikinsu har da na 'yan kabilar Igbo. Shugaban kabilar Igbo yace sun ji dadi sai dai an takaita tafiya da irin wuraren da zasu je ba kamar yadda aka saba yi ba. Duk da haka sun godewa Allah domin ya basu rai. Suna addu'a a samu zaman lafiya. Wani shugaban Jere shi ma ya yiwa Allah godiya da aka samu aka yi hidimar sallah.
An gudanar da bukukuwan sallah ne tare da hana ababen hawa zirga-zirga musamman na haya har tsawon kwana uku domin tsaro.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.