Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan kasar Belgium sun kara kama mutane dangane da harin Brussels


'Yansandan Belgium yayinda suke kai samame
'Yansandan Belgium yayinda suke kai samame

‘Yansandan kasar Belgium sun bayyana wadansu sababbin kame kame, da kuma kai sumame jiya Talata, dake da alaka da hare haren da aka kai a Brussels da kuma Paris, yayinda ma'aikatan gidan kaso suke

bayyana damuwa kan yadda za a tunkari nasarorin da suke samu na kula da mutanen da ake ci gaba da kamawa.

An tuhumi wadansu karin mutane biyu da ake kira Smail F da Ibrahim F da laifin ta’addanci da kisan kai dangane da hare haren da aka kai a Brussels da suka yi sanadin mutuwar mutane 32. Masu shigar da kara na kasar Belgium sun sanar a kafofin sadarwar kasar cewa, mutane biyun wa da kani ne.

‘Yan sandan Brussels sun kuma tsare wadansu mutane uku bayan gudanar da bincike a gidajensu dake babban birnin lardin Uccle.

Ba a yi wani karin haske dangane da tsare mutanen ba, sai dai kafofin sadarwar kasar Kenya sun yayata cewa, alkali zai yanke hukumci yau Laraba kan ko za a ci gaba da tsare mutanen uku.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG