Mahukuntan Belgium sun gano madugun shirya hare-haren da aka kai kan Paris babban birnin Faransa, Salah Abdeslam.
Ranar 13 ga watan Fabrairun bara ne aka kai harin da ya hallaka mutane fiye da 130 kuma bayan harin Salah Abdelsam ya yi batar dabo, ya bace babu sawunsa lamarin da ya jawo sabuwar barazana ya tada wa nahiyar turai hankali ainun.
Masu bincike suna neman wani dan shekaru 24 da haihuwa dan kasar Belgium mai suna Najim Leachraoul amma yana da wani sunan da yake anfani dashi wato Soufiane Kayal. Shi ma yana kan gudu, ba'a san inda yake ba.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishin masu shigar da kara na gwamnatin tarayyar Belgium shi Najim ya je Syria a shekarar 2013. Yayinda 'yansanda ke bincike sun gano DNA dinsa cikin hare-haren.
Kamar yadda mahukuntan Faransa da na Belgium suka shaidawa kafofin labarai an samu DNA dinsa cikin bamabaman da aka yi anfani dasu.
Haka ma hukumomi sun ce mutum na uku da aka kashe cikin sammamcin da aka kai makon jiya dake da sunan batar da kama watao Samir Bouzid amma sunansa na gaskiya Mohamed Bekaid ne.
Samun cafke Salah Abdeslam da hukumomi suka yi ranar Juma'a da ta gabata zai taimaka wurin kawo haske kan abubuwan da har yanzu suna cikin duhu.
Wani kuma da hukumomin ke nema ruwa a jallo shi ne Mohamed Abrini dan shekaru 31 da haihuwa. Ana kyautata zato yana tare da Abdeslam a cikin wata bakar mota da aka gano a arewacin birnin Paris bayan hare-haren.
An kama Abdeslam tare da wasu mutane hudu a Brussels a anguwar Molenbeek inda ya girma. Lauyansa yace zai yi adawa da kaishi Fransa domin ya fuskanci hukunci