Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da Suka Dasa Bama Bamai A Filin Jirgin Brussels


‘Yan sanda a kasar Belgium sun bayarda sanarwar neman wani mutum dangane da harin bam da aka kai yau kan filin jirgin saman birnin Brussels, daya daga cikin hare-haren da kungiyar ISIL ko Da’esh ta dauki alhakin kaiwa a babban birnin, har mutane akalla 30 suka mutu.

Hare-haren, tare da wani a tashar jiragen karkashin kasa dake kusa da nan, sun kuma raunata mutane 130.

Kamfanin dillancin labarai na kungiyar Da’esh mai suna Amaq, ya ce mahara sun bude wuta a cikin filin jirgin kafin su tayar da bama-baman dake kunshe cikin jigidar da suke rataye da ita, yayin da wani dan harin na kunar bakin wake ya kai farmaki kan tashar jiragen karkashin kasa ta Maalbeek. Wani jami’in Amurka yace babu wata hujja ta yin shakkar wannan ikirari na kungiyar Da’esh.

Firayim minister Charles Michel na Belgium ya bayyana wannan lokaci a zaman na alhini ga kasar, yana mai kira ga dukkan al’umma da su kwantar da hankula su kuma nuna kaunarsu ga juna.

A lokacin wani jawabin da yayi a Havana, babban birnin Cuba, shugaba Barack Obama na Amurka yace Amurka zata yi duk abinda ya kamata ga kawarta Belgium, domin hukumta wadanda suka aikata wannan abu. Shugaban yace Amurka tana tsaye daram a bayan Belgium da ta fuskanci wadannan hare-hare na rashin mutunci a kan mutanen da basu jib a, basu kuma gani ba.

Hotunan bidiyo sun nuna mutane suna gudu daga filin jirgin saman Brussels yayin da fashe fashe har sau biyu suka ragargaza manyan tagogin ginin, hayaki kuma yana fita waje da misalign karfe 8 na safiya agogon kasar. Kafofin labaran kasar sun ce an samu bam na uku wanda bai tashi ba. Kafofin labarai dabam dabam sun ce mutane akalla 11 suka mutu a fashe fashen bama bamai na filin jirgin saman.

Wani mai gabatar da kara na Belgium yace akalla daya daga cikin hare-haren na kunar bakin wake ne. Wani jami’in tsaro na Turai yace an samu wata bindiga, ko kuma dai guda biyu kirar Kalashnikov a wurin da aka kai harin na filin jirgin sama.

Magajin garin birnin Brussels yace an kashe mutane akalla 20, wasu 55 sun ji rauni jim kadan bayan nan a wata tashar jiragen karkashin kasa dake kusa da hedkwatar KTT.

A halin da ake ciki, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen yin Allah wadarai da hare haren na Brussels. Shugaba Buhari, yace Najeriya, wadda ita ma ta fuskanci hare-haren ta’addanci na shekara da shekaru, tana mai mika jaje tare da nuna goyon bayanta ga gwamnati da kuma al’ummar Belgium kan wannan abu.

Shugaba Buhari yace wadannan hare-hare na Brussels sun kara karfafa bukatar hada kai tsakanin kasashen duniya wajen fuskanta da kuma ragargaza ta’addanci da ‘yan ta’adda a duniya.

XS
SM
MD
LG