Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan ISIS na yunkurin canza salon kai hari a Syria da Iraqi


Hafiz Saeed yana daya daga cikin shugabannin ISIS
Hafiz Saeed yana daya daga cikin shugabannin ISIS

Jami’an tsaron da ke aiki ba ji ba gani don karya lagon yaduwar ta’addanci zuwa cikin Turai na shinshino yiwuwar cewa mayakan sunkurun na kokarin canza dabarar kai muggan hare-hare ga muhimman wurare da manyan gine-ginen gwamnati a Syria da Iraki.

Bisa la’akari da bayyanar na’urar kwamfutar da aka tsinta a cikin bola a Belgium a lokacin samamen ‘yan sanda bisa alaka da harin bam da aka kai a garin, wacce take dauke da hotunan ofishin Firaministan kasar.

Tare da shedar data bayyana, hakan na nuna cewa, ‘yan kunar bakin waken ya da kani da suka kai harin Khalid da Ibrahim Bakraoui, sun aiwatar da liken asiri akan faifan bidiyon da ke nuna ma’aikatar Nukiliyar Belgium ta Tihange.

Wannan na nuna alamar cewa, ‘yan ta’adda na da niyyar canza salon kai hari ga wurare masu saukin kamar tashoshin jama’a da shaguna, zuwa kan manyan muhimman wuraren gwamnati.

Wani mayakin sa kai na ISIS
Wani mayakin sa kai na ISIS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG