Tun farko, jami’ai sun ce mutane 35 aka kasha. An sami kuskuren ne sabili da kirga wadansu mutane uku da aka yi sau biyu wadanda suke da takardar izinin zama ‘yan kasa a kasashen biyu.
An tantance dukan wadanda aka kashe a tagwayen hare haren, da suka hada da ‘yan asalin kasar Belgium goma sha bakwai, da ‘yan kasashen ketare 15, bisa ga cewar Ine Van Wymersch kakakin ofishin babban mai shigar da kara na kasar Belgium.
Hukumomi sun ce a kalla mutane casa’in har yanzu suna kwance a asibiti, sama da arba’in kuma a dakin gobe da nisa.
A halin da ake ciki kuma, Amurka tace, tilas ne a kara daukar mataki dangane da musayar bayananan sirri a kasashen turai, biyo bayan hare haren ta’addancin da aka kai a birnin Brusels da suka haddasa asarar rayuka.
Kakakkin fadar White House Josh Earnest yace hare haren da aka kai tashar jiragen sama da ta kasa a Brussels matashiya ce, kan muhimmancin bin diddigin bayanan leken asiri.
Ya jadada cewa, Amurka tana goyon bayan Belgium yayinda take gudanar da bincike.