Masu gabatar da kara sun ce an raunata akalla mutum guda yayin wannan samamen.
An kaddamar da 19 daga cikin samamen ne a ciki da bayan birnin na Brusselss.
Ana kyautata zaton Abdulsalam ya ketara zuwa Belgium ranar 14 ga watan Nuwamba, 'yan sa'o'i bayan da 'yan ISIS su ka kashe mutane 130 su ka kuma raunata wasu da dama a wasu shiryayyun hare-hare a birnin Paris.
An hallaka wanda ake zargi da jagorantar hare-haren, Abdelhamid Abaaoud ranar Laraba a wani samamen da 'yan sanda su ka kai arewacin bayan birnin Paris.
Zuwa yau Litini, tasoshin jiragen kasa da makarantun Belgium sun ci gaba da kasancewa a rufe, yayin da mazauna birnin ke fuskantar rana ta uku cikin tsauraran matakai da kuma wani makon da harkokin tsaro su ka mamaye komai.
Da daddare a birnin Paris, jami'an tsaro dauke da muggan makamai, sun yi ta sintiri a titunan da akasari babu kowa ciki, yayin da birnin ke kokarin murmurewa daga kashe-kashen da ya faru.
Kafafen yada labarai a Belgium sun ce 'yan sanda sun damke wasu mutane hudu a daren ranar Asabar, daya daga cikinsu ma ana tsammanin ya yi guru da bama-baman kunar bakin wake.