Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dakarun Nijar 10 A Wani Sabon Harin Ta'addanci


Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

Wani harin ta’addancin da aka kai a kauyukan jihar Tilabery da ke Nijar ya yi sanadin rasuwar jami’an tsaro da dama a lokacin da suke kokarin kwato tarin shanu da maharan suka sace a karkarar Anzourou.

NIAMEY, NIGER - Kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani akan wannan al’amari ba amma wasu majiyoyi na cewa an halaka ‘yan ta’adda da dama.

Dumbin ‘yan bindigar da ke kan babura ne suka afkawa garuruwan da suka hada da Doukou Sarahou da Doukou Makani da kuma Doukou Koirategui na karkarar Anzourou a yammacin ranar Lahadi a kokarinsu na fatattakar ilahirin garken shanun jama’a.

Sanar da jami’an tsaro ke da wuya suka bi sawun ‘yan bindiga domin kwato dabbobin da suka sata sai dai kuma askarawan na Nijar sun yi kicibus da su a wani wurin da suka masu kwanton bauna inda aka dauki lokacin mai tsawo suna gwabzawa.

Yunkurin jin ta bakin Shugaban da’irar Anzourou ya ci tura domin wayarsa a kashe take.

Amma alkaluman kafar labaran al’amuran soja ta Info Militaires na cewa jami’an tsaron Garde Nationale 10 ne suka kwanta dama wasu hudu suka yi rauni sanadiyar wannan al’amari, yayinda suka yi nasarar kwato dabbobin da aka sace tare da karkashe dimbin ‘yan ta’addan da kawo yanzu ba a bayyana adadinsu ba.

Kungiyoyin ta’addancin yankin Sahel da ke da sansani a wasu sassan kasashen Mali da Burkina Faso sun zafafa kai hare-hare a ‘yan kwanakin nan a jihar Tilabery abinda wasu ke alakantawa da matakin janye jami’an tsaro daga wasu sassan jihar don karfafa matakan tsaro a birnin Yamai, sakamakon barazanar amfani da karfin sojan da kungiyar CEDEAO ta ayyana a rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Ko da yake, wasu ‘yan Nijar na fassara wannan yanayi na tabarbarewar tsaron a matsayin wani makircin da suke zargin Faransa ta kullawa don bata sunan Majalisar soja ta CNSP a idon ‘yan kasa.

Shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou wanda ya nuna damuwa da abubuwan dake faruwa na mai shawartar mahukunta da al’umma kan maganar hada kai.

A wani labarin da ke da nasaba da dambarwar siyasar da ake ciki a Nijar Majalisar soja ta CNSP ta musanta labarin da ke cewa ta bukaci ECOWAS ta shigar da tsohon Shugaban Nijar Issouhou Mahamadou a jerin wadanda za a tattauna da su a zaman sulhun da aka sa gaba.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Dakarun Nijar 10 Sun Rasu Sakamakon Wani Harin Ta'addanci A Karkarar Anzourou.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG