Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Hare-haren Ta'addanci Suka Karu A Jihar Tilabery Tun Bayan Juyin Mulkin Soji A Nijar


Jihar Tilabery A Nijar
Jihar Tilabery A Nijar

Masu fashin kan sha'anin tsaro sun ce matsalar hare-haren na da alaka da tsamin dangantaka da aka samu tsakanin Nijar da Faransa bayan juyin mulkin da aka yi.

NIAMEY, NIGER - Ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar cewa wani harin kwanton-bauna da ‘yan ta’adda suka kitsa a kauyen Koutougou da ke tsakanin garurwan Boni da Torodi a jihar Tilabery ya yi sanadin rasuwar sojoji da dama tare da jikkata wasu sama da 20.

Ko da yake, dakarun gwamnatin sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda 100 lamarin da ya farfado da mahawwara a tsakanin al’umma dangane da yadda sha’anin tsaro ke kara tabarbarewa a ‘yan makwannin nan.

Lamarin ya wakana ne a wajejen karfe daya da rabi na ranar jiya talata lokacin da wani ayarin motocin sojoji ya fada tarkon ‘yan ta’dda dab da kauyen Koutougou da ke a tazarar km 52 a kudu maso yammacin Torodi kan hanyar garin Boni a cewar sanarwar ofishin Ministan tsaron kasa wacce ta kara da cewa a yayin wannan arangama sojojin Nijar sun yi nasarar halaka ‘yan ta’adda sama da 100 da ke kan babura.

Ko da yake, sojoji 17 sun rasu yayin da wasu akalla 20 suka ji rauni wadanda suka hada da 6 da ke cikin mawuyacin hali da tuni aka kwantar da su a asibitin birnin Yamai.

Wannan shi ne karo na bakwai da ake fuskantar hare-hare a jihar Tilabery tun bayan da soja suka yi juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli, lamarin da masu fashin baki ke dangantawa da wasu tarin dalilai.

Jigo a jam’iyar PNDS ta Shugaba Mohamed Bazoum, Idrissa Waziri na cewa halin da aka shiga a yau a yankin Tilabery na nuna wa a fili yadda juyin mulkin 26 ga watan Yuliy ya bai wa ‘yan ta’adda damar walwala sakamakon janye shingayen tsaron da ake da su a baya.

Amma mai fashin baki kan sha’anin tsaro Abbas Moumouni na mai alankata yawan hare-haren na ‘yan kwanakin nan akan yanayin tsamin dangantakar da aka shiga a tsakanin Faransa da Nijar tun bayan kifar da Gwamnatin farar hula.

Wannan ya sa Shugaban kungiyar kulawa da rayuwa, Hamidou Sidi Fody ke gargadin kasashen iyakoki uku da su farfado da ayyukan tsaro na hadin guiwa.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an kara fuskantar wasu hare-haren na daban a cikin daren jiya a jihar ta Tilabery wadanda kawo yanzu ba mu samu bayanai a hukunce ba da ke tabbatar da faruwar su in ban da muryoyin mazaunan wasu kauyukan yankin da ake yadawa ta kafafen sada zumunta, cikin yanayin zullumi suna neman dauki.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Hare-haren Ta'addanci Sun Karu A Jihar Tilabery Tun Bayan Juyin Mulkin Soja A Nijar.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG