Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sojojin Nijar Sun Mutu A Hatsarin Mota A Lokacin Da ‘Yan Ta’adda Suka Kai Wani Hari


Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

Ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar sojojin kasar kimanin 5 sanadiyar hatsarin mota a  dai dai lokacin da wani harin ta’addancin da aka kai a madatsar Kandaji da ke jihar Tilabery ya hallaka wasu sojoji 7, sannan wasu 7 suka ji rauni.

NIAMEY, NIGER - Lamarin ya faru ne a yayin da aka yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda sama da 100 abin da ya sa masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suka gargadi mahukuntan kasashen Sahel akan bukatar tsauraran matakan hadin gyiwa a karkashin kungiyar AES da suka kafa a baya-bayan nan.

A ranar Alhamis ne daruruwan ‘yan bindiga akan babura suka afka wa jami’an rundunar Almahaou da ke aikin tsaron wurin da ake gudanar da ayyukan ginin madatsar ruwa ta Kandaji wacce ta hanyarta Nijar ke hangen samar da wadatar wutar lantarki da kuma bunkasa ayyukan noma.

Sanarwar ofishin ministan tsaro ta yi nuni da cewa jajircewar askarawan kasar a yayin wannan gumurzu ta sa ‘yan ta’addan arcewa ba shiri, koda yake lamarin ya haddasa mutuwar soja 7 kuma wasu 7 suka ji rauni har aka kwantar da su a asibitin sojoji.

Sanarwar ma’aikatar tsaron ta kara da cewa ayarin motocin kai dauki da aka tura da zummar karfafa wa sojojin kasar guiwa ya yi hatsari akan hanya, abin da ya yi sanadin rasuwar kimanin 5 daga cikinsu.

Bayan wannan ne jiragen Nijar suka yi luguden wuta akan maharan a kewayen kauyen Tijiane da ke a tazarar kilomita 20 a Arewa maso gabas da garin Ayorou, wato kusa da iyakar Mali ta bangaren Nijar inda ‘yan ta’adda fiye da 100 ne aka kashe tare da lalata baburansu da makamai sakamakon wannan lugude.

Matsalolin tsaro na daga cikin dalilan da sojojin CNSP suka ayyana a matsayin hujojin da suka fake da su don kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, to sai dai da alama har yanzu da sauran rina a kaba bisa la’kari da abubuwan da suka wakana a ‘yan makwannin nan a yankin na Tilabery mai makwaftaka da Mali da Burkina Faso kasashen da masu bin diddigin al’amuran yau da kullum ke cewa Nijar ta yi masu fintikau akan maganar tabbatar da tsaro ganin yadda ‘yan ta’adda suka mamaye masu yankuna da dama.

A baya bayan nan kasashen uku sun cimma yarjejeniyar taimakawa juna a fannin tsaro a karkashin wata kungiyar da suke kira AES.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Wasu Sojojin Nijar Sun Mutum A Hatsarin Mota A Lokacin Da ‘Yan Ta’adda Suka Kai Wani Hari.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG