Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Kasar Zimbabwe Ta Nemi Tallafin Najeriya.


Zimbabwean Chief of Army Staff inspects a guard of honor by Nigerian Airforce
Zimbabwean Chief of Army Staff inspects a guard of honor by Nigerian Airforce

Hafsan Hafsoshin sojojin saman Zimbabwe Air Marshal Elson Moyo ya bukaci rundunar sojojin Najeriya ta tallafawa rundunar kasar ta Zimbabwe a yayin da ya Ziyarci hedkwatar sojojin saman Najeriya.

Air Marshall Moyo yace lalle suna bukatar taimakon sojin saman Najeriya wajen gyara jiragen yakinsu samfurin F7 da Mi35 wadanda Najeriya ita ma tanada irinsu kuma tana fafatawa dasu yakin da takeyi da yan ta’adda.

Bugu da kari, kasar ta Zimbabwe na neman Mayakan saman Najeriyar su tallafa mta a fannin fasahar Kurman jirgin nan maras matuki da kuma fannin bincike.

Babban Hafsan saman na Zimbabwe yace cikin lokaci kankani, Najeriya ta cimma gagarumar nasara wajen samarwa da kuma bunkasa fasaha a cikin gida a fannin jiragen yaki, abin ma kenan da yasa suka zo da kokon bara don neman agaji.

A jawabinsa, Babban Hafsan Hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Oladayo Amao ya bayyana cewa, a shirye suke su hada kai da Zimbabwen don a taimaka mata.

Air Marshall Amao yace bunkasa lamuran aiki tsakanin kasashen Afrika ka iya zama silar shawo kan kalubalen tsaro dake addabar nahiyar.

Amao yace hadin kai a fannonin horo da musayar fasaha zai karfafa karfin dogaro da kai tsakanin mayakan nahahiyar Afrika.

Hafsan mayakan na Zimbabwe a halin yanzu yana ziyaar aiki na tsawon mako guda a Najeriya, inda ake sa ran ya ziyarci rundunonin mayakan saman Najeriyar da kuma shiyyar Arewa maso gabashin Najeriyar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG