Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Nasarawa na Zargin Dan Jarida


'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya

Yayin da mata a koina a Najeriya ke cigaba da gangami a sassa daban daban dangane da daliban da aka sace, a jihar Nasrawa 'yan sandan jihar sun gurfanar da wani dan jarida a gaban kotu domin ya rubuta rahoto inda ya nuna 'yan sanda mata sun shiga gangamin da mata 'yan uwansu suka yi.

Har yanzu mata da kungiyoyi suna cigaba da yin gangami a jihohin Najeriya inda na jihar Nasarawa ya dauki wani salo daban.

A jihar Nasarawa hukumar 'yan sandan jihar ta kai wani dan jarida kara kotu bisa ga rahoton da ya buga na cewa wasu jami'an tsaro mata sun shiga gangamin da matan jihar suka yi akan 'yan matan nan da aka sace a Chibok dake jihar Borno.

Dan jaridar mai suna Joseph Fir dake aiki da jaridar Daily Trust ya buga labari ne akan gangami da addu'o'i da matan jihar Nasarawa Musulmi da Kirista suka yi akan matsalolin tsaro a kasar da kuma sace 'yan matan Chibok.

Da ya ke yiwa wakiliyar Muryar Amurka bayani Zainab Babaji, Joseph Fir yace ranar Alhamis da ta wuce matan jihar Nasrawa da wasu kungiyoyin mata da wasu mata 'yan sanda sun shiga gangami inda suka yi addu'o'i na musulunci da kiristanci. Lokacin gangamin yace ya zanta da 'yan sanda mata domin ya tabbatar 'yan sanda ne. Bayan ya buga rahoton sai kwamishanan 'yan sandan jihar ya kirashi yace ya fada masu suna 'yan sanda mata da suka shiga gamgamin. Da yaki sai suka kulleshi tun daga safe har zuwa karfe tara na dare. Bayan an yi belinsa sai kuma suka kai kararsa gaban kotu.

Jami'in 'yan sandan mai hulda da jama'a ASP Ismaila Umar yace dan jaridan ya batawa 'yan sandan jihar suna. Yace kungiyar musulmai mata da na kirista suka nemi izinin su yi gangami akan daliban da aka sace. Bayan gangamin rahoton da dan jaridar ya rubuta ya nuna cewa 'yan sanda mata sun shiga cikin gangamin wanda kuma ba haka ba ne. Sun nemi ya bayyana masu 'yan sanda matan da suka shiga cikin gangamin amma ya ki. ASP Ismaila Umar ya musanta zargin cewa sun kama 'yan sanda matan da suka shiga gangamin. Ya dage cewa sun gurfanar da Joseph Fir gaban kotu domin rahotonsa ba gaskiya ba ne. Suna neman kotu ta wankesu.

Amma shugaban kungiyar 'yan jarida ta Najeriya reshen jihar Nasarawa Dan Yakubu ya bayyana takaicinsa yadda 'yan jarida da jami'an tsaro zasu je gaban kuliya. Yace 'yan jarida da jami'an tsaro aiki daya su keyi.

Ga rahoton Zainab Babaji.
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG