Gwamnan ya bayyanawa manema labarai cewa yan matan da aka sace ranar 14 ga watan Afirilu suna cikin bidiyon da 'yan Boko Haram suka nuna. Sanarwar ta samu sa hannun mai baiwa gwamnan shawara akan harkokin sadarwa Alhaji Isa Umar Gusau.
A cikin bidiyon an gano yara mata guda hamsin da hudu da sunayensu. Dama shugaban kungiyar ta Boko Haram wanda yake kiran kansa Abubakar Shekau shi ya dauki alhakin sacesu.
An gano sunayen yaran ne da taimakon daliban makarantar da suka kubuce daga hannun 'yan bindigan lokacin da suka sacesu. Haka ma iyayen wasu daga cikin yaran su ma sun taimaka. Haka ma malamansu sun gano fuskokin yaran bayan sun kalli faifan bidiyon tare da gwamnan.
Yanzu dai gwamnatin jihar Borno ta wallafa sunayen 'yan mata hamsin da hudu da aka gano a cikin bidiyon domin tabbatarwa jama'a cewa 'yan matan dake bidiyon suna cikin daliban Chibok.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.