Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Fito da Bidiyo Dauke da Mata


 Wasu daga cikin 'yan matan da aka sace a cibok an dauki wanna hoto,12, ga Mayu 2014.
Wasu daga cikin 'yan matan da aka sace a cibok an dauki wanna hoto,12, ga Mayu 2014.

A wani sabon bidiyo da mutumin da yace shine shugaban kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, ya fitar a baya-bayannan, Abubakar Shekau yace ya musuluntar da wadannan mata, wadanda yace ya sato su, sannan yana bukatar ayi musaya dasu.

Matan su sama da 100 wadanda ke sanya da hijabai, sun jeru a cikin wani waje kamar daji, inda sukayi ta karatun Qur'ani. Mr. Shekau ya bukaci a sauya masa matan da fursunoninsa da aka kama.

A cikin bidiyon anyi hira da uku daga cikin ‘yan matan inda biyu daga cikin sukace su mabiya addini kirista ne amma sun musulunta, ita ta uku dama musulmace, koda yake sun ce ba cutar dasu ba.

Baza mu iya tantance lokaci da aka dauki wanna bidiyo ba, amma a cikin ana iya ganin wani dan bindiga rike da kyamara yana daukan bidiyo.

Boko haram sun dade sun addabar arewacin Najeriya tun shekaran 2009 inda suka kashe mutane da dama suka kuma kona gidajen da wuraren sana’a da wuaren ibada.

Sashen Hausa na Muryar Amurka na kokarin bincikawa domin tabbatarwa ko wadannan sune daliban Cibok da aka sace.

Manya-manyan Malaman Musulunci a Najeriya da ma duniya sunyi Allah Wadai da satar daliban Cibok, suna cewa aikin ta'addanci bata addinin Musulunci ne, kuma tauye hakkin bil adama ne.

Ya zuwa yanzu, hukumomin Najeriya basu mayar da martani akan wannan sabon bidiyo ba.
XS
SM
MD
LG