Kungiyar Boko Haram ta nemi gwamnati ta sako 'yan kungiyarta dake tsare kana ita ma ta sako 'yan mata guda dari cikin wadanda ta tsare. Mark Omeri shugaban wata cibiya ta hadin gwiwa da gwamnatin tarayya ta kafa domin yiwa kasa bayanai yace suna son kowa ya sani cewa duk abun da ya dace da duniya keyi cikin irin wannan halin gwamnatin kasar zata yi. Yace duk matakan da suka kamata a dauka za'a dauka.
Mr. Omeri yace nufin gwamnatin Najeriya ne a sako 'yan matan lami lafiya ba tare da wasu sharuda ba. Da wakiliyar Muryar Amurka tace masa a kasashe kamar su Afghanista, Pakistan , Israila da Sudan Ta Kudu an yi irin wannan musayar sai yace 'yan kungiyar Boko Haram dake tsare ba firsinonin yaki ba ne. Wadannan 'yan Najeriya ne wadanda suka shiga wani hali. Ana tsare da su ne domin a taimaka masu su fita daga halin hallaka mutane da aikata ta'adanci.
Mai magana da yawun hukumar SSS tace 'yan Boko Haram na yanzu sun zama 'yan kasuwa. Tace kowa ma yana iya zama dan Boko Haram. Tun bara aka kashe Abubakar Shekau na ainihi da Abu Kaka na ainihi.
Shi kuwa shugaban hadakar kungiyoyin kwadago ta kasa Bobai Foigama yayi gargadi game da shirin hadin gwiwa da Najeriya ta shiga da kasashen Amurka, Biritaniya, Faransa da kuma Israila domin kwato 'yan matan da aka sace. Yace wasu cikin kasashen da suka kawo mana doki tuni suka yi harsashen kasar zata tarwatse a shekarar 2015. Sabili da haka kada Najeriya ta saki jiki da su. Gwamnati ta sa masu idanu sosai domin kada su saci sirin kasar na gudanar da tsaro.
Ga rahoton Medina Dauda.