A cikin wasikar da suka baiwa gwamnan jihar Ibrahim Geidam a birnin Damaturu matan sun nuna alhinisu akan cigaba da tsare 'yan matan a dajin Sambisa da kungiyar Boko Haram ke yi.
Hajiya Halima Joda shugabar kungiyar ta jihar Yobe tace sakon da suka baiwa shi mai girma gwamnan jihar domin a kaiwa gwamnatin tarayya suna roko ne domin fadan ya wuce abun da za'a fito a yi yaki akai. A matsayinsu na iyaye suna roko ne da cewa gwamnatin tarayya da na jihohi da duk wadanda zasu fada a ji su hada hannu su taimakesu a sako masu 'ya'yansu.
Dangane da bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar Hajiya Halima Joda tace bidiyon ya kara tayar masu da hankali domin gasu suna gani amma ba zasu iya mika hannunsu su karbesu ba. Tace su nasu yanzu lallashi su keyi. A kungiyance suna ganin lallashi ne mafita. Fito na fito ba zai haifar da da mai ido ba. Idan an yi fito na fito ana iya rasa wasu 'yan matan.
Kungiyar matan 'yan jarida na jihar Yobe ba'a barta baya ba. Kungiyar ta shiga gangamin. Kungiyar tana bin kananan hukumomi tana fadakar da mutane domin a tashi a yi taimako.
Ga cikakken rahoto gada Sa'adatu Fawu.