Wani kwararre akan sha’anin tsaro, kuma dan yankin na Borno, Malam Hussaini Monguno, yana ganin wannan tayin da suka yi abun dubawane, domin a kawo kashen wannan rigima, a cikin ruwan sanyi.
Yace "ya danganta da wanene yayi wannan tayin idan jigo ne a cikin wannan ‘yan kungiyar ya fada kuma inda gaske suke, in an kama mutanen su suna kurkuku in kuma ba’a filin daga aka kamasu ba yakamata tunda ba’a kaisu gaban sharia ba in dai har da gaske ne suka yi wannan tayi yakamata su sake mutanen nasu in yaso suma su bada yaran nan gaskiya in hakan za’a yi gwamnati ta kafa kwamiti na gaggawa aduba wannan tayin.”
Mallam Hussaini ya kara da cewa “yakamata a nemi dattawa na kirki gwamnati ta sasu a kwamiti a nemi mutane nan a zauna dasu in dai har zasu sako yaran nan in akwai mutanen su da aka kama wadanda bazu da laifi kaiwa an kamasu ne don suna boko haram, bada bindiga aka kamasu ba, ba wani laifi akayi ba sai a tantance a sake su, suma su bada yaran.”
Ya zuwa yanzu jama'ar Najeriya da duniya na zuba idanu wajen ganin irin matakan da za'a bi, domin mayar da dalibannan wajen iyayensu.